Friday 30 December 2016

Maganin Bakin Ciki

Al-Imam Ibnul Kayyim ya ambaci wasu magunguna a cikin littafinsa Zadul Ma’ad wadanda suke warkar da bakin ciki da damuwa da zullumi. Ga su a takaice:
  1.  Tauhidi
  2. Imani cewa Allah ba zai zalunci bawanSa ba ko ya kama shi da laifin da bai aikata ba.
  3. Bawa yayi ikrari (daga ciki har waje) cewa shine ya zalunci kansa.
  4. Neman tsani zuwa ga Allah da mafi soyuwar abubuwa gareShi. Sune kuwa sunayenSa da sifofinSa. Kuma sunayen da suka fi tarowa ga dukkan ma’anonin sunayenSa da sifofinSa sune, Al-Hayyu da Al-Kayyumu.
  5.  Neman taimako wajen Allah Shi kadai.
  6. Kwadayin abun da ke wurin Allah.
  7. Dogaro da Allah da maida al’amurra gareshi da kuma ikrari cewa matukarsa tana hannun Allah wanda Yake juyata yadda Yake so, tare da tabbatar da cewa dukkan abun da Allah Ya hukunta masa shine mai gudana, kuma hukuncinSa adalci ne.
  8.  Zuciyarsa ta rika kiwo a dausayoyin Alkurani. Ya yi amfani da Alkurani a matsayin fitila a duk lokacin da ya samu kansa a cikin duffai na sha’awa ko shakka.
  9. Istighfari.
  10.  Tuba
  11. Jihadi
  12. Sallah.
  13. Imani da kuma tabbatarwa a baka cewa tsiminsa da dabararsa basu kubutar da shi sai da taimakon Allah. (لا حول و لا قوة إلا بالله)